A A A A A

Luka 18:1-23
1. Yesu ya faɗa wa almajiransa wani misali, don ya koya musu yadda ya kamata su dinga yin adduʼa kullum, ban da fasawa.
2. Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba.
3. A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, ‘Ka ba ni adalci tsakanina da maƙiyina.’
4. “An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba,
5. amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada ta gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ”
6. Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce.
7. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne?
8. Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma saʼad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”
9. Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane, ya ce,
10. “Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin adduʼa. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji.
11. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi adduʼa game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan.
12. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’
13. “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’
14. “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”
15. Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don ya taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su.
16. Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa, ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.
17. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”
18. Wani mai mulki ya tambayi Yesu, ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
19. Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, babu wani managarci, sai Allah kaɗai.
20. Ka san dokoki da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”
21. Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”
22. Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, saʼan nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”
23. Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai.