A A A A A

Luka 17:20-37
20. Wata rana, Farisiyawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai zo, Yesu ya amsa, ya ce, “Ai, mulkin Allah ba takan zo ta wurin yin ƙallon ku ba.
21. Mutane kuma ba za su ce, ‘Ga shi nan,’ ko kuma, ‘Ga shi can’ ba, domin mulkin Allah yana cikinku ne.”
22. Sai ya ce wa almajiransa, “Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.
23. Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin bin su.
24. Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa.
25. Amma da fari, dole ya sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi.
26. “Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum.
27. Mutane suna ci, suna sha, suna auraya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Saʼan nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.
28. “Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine.
29. Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka.
30. Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana.
31. A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don ya kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada ya koma don wani abu.
32. Ku tuna fa da matar Lot!
33. Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi.
34. Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.
35. Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.
36. (Maza biyu za su kasance a gona, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan).”
37. Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”