A A A A A

Luka 17:1-19
1. Yesu ya ce wa almajiransa, “Dole ne a sami abubuwa da suke sa mutane su yi zunubi, amma kaiton mutumin nan wanda suke zuwa ta wurinsa.
2. Gwamma a ɗaura dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku, da ya sa ɗaya daga cikin ƙananan yaran nan ya yi zunubi.
3. Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗanʼuwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa.
4. In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”
5. Sai manzannin suka ce wa Ubangiji, “Ka ƙara mana bangaskiya!”
6. Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.
7. “In ɗaya a cikinku yana da bawa, wanda yake masa noma, ko kiwon tumaki, da dawowar bawan daga gonar, ai, ba zai ce masa, ‘Ka zo nan, ka zauna, ka ci abinci ba?’
8. Ashe, ba zai ce masa, ‘Ka shirya mini abincin yamma, ka shirya ka yi mini hidima domin in ci in sha, bayan haka kana iya ci, ka kuma sha ba?’
9. Shin, zai gode wa bawan don ya yi aikin da aka ce ya yi ne?
10. Haka ku ma, bayan kun yi duk abin da aka ce muku ku yi, ya kamata ku ce, ‘Mu bayi ne marasa cancanta, mun dai yi aikinmu ne kaɗai.’ ”
11. Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi takan iyakar Samariya da Galili.
12. Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa,
13. suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!”
14. Da ya gan su sai, ya ce, “Ku je ku nuna kanku ga firistoci.” Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtace.
15. Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya.
16. Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.
17. Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Ba duka goma ne aka tsabtace ba? Ina sauran taran?
18. Ba wanda ya dawo don ya yabi Allah, sai dai wannan baƙon?”
19. Sai ya ce masa, “Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai. ”