A A A A A

Luka 15:1-10
1. Yanzu fa, masu karɓar haraji da “masu zunubi” duka suna taruwa don jin koyarwar Yesu.
2. Amma Farisiyawa da malaman dokoki suka yi gunaguni, suna cewa, “Wannan mutum yana karɓan ‘masu zunubi,’ kuma yana ci tare da su.”
3. Sai Yesu ya faɗa musu wannan misali, ya ce,
4. “In ɗayanku yana da tumaki ɗari, saʼan nan ɗayansu ta ɓace. Ashe, ba zai bar tasaʼin da tara a fili ya je neman wadda ta ɓace, har sai ya same ta ba?
5. In ya same ta, zai sa ta a kafaɗa da murna,
6. ya dawo gida. Saʼan nan zai kira abokansa da maƙwabtansa wuri ɗaya, ya ce, ‘Ku taya ni murna, na sami tunkiyana da ta ɓata.’
7. Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasaʼin da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.
8. “Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, saʼan nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za ta ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba?
9. In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’
10. Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban malaʼikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”