A A A A A

Luka 6:27-49
27. “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na: Ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri.
28. Ku albarkaci waɗanda suke laʼanta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku adduʼa.
29. In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ʼyar cikin ma.
30. Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yǎ mayar maka.
31. Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.
32. “In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko ‘masu zunubi’ ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu.
33. In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko ‘masu zunubi’ ma suna yin haka.
34. In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyanka ne kawai, ina ribar wannan? Ko ‘masu zunubi’ ma, suna ba da bashi ga ‘masu zunubi’, da fata za a biya su tsab.
35. Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ʼyaʼyan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.
36. Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.
37. “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku.
38. Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yǎ yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”
39. Ya kuma faɗa musu wannan misali, cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba?
40. Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.
41. “Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗanʼuwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba?
42. Yaya za ka ce wa ɗanʼuwanka, ‘Ɗanʼuwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, saʼan nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗanʼuwanka.”
43. “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ʼyaʼya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ʼyaʼya masu kyau.
44. Kowane itace da irin ʼyaʼyansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ʼyaʼyan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ʼyaʼyan inabi daga sarƙaƙƙiya.
45. Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”
46. “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa?
47. Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yǎ ji kalmomina, yǎ kuma aikata.
48. Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, saʼan nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.
49. Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A saʼad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yǎ rushe, mummunar rushewa kuwa.”