English
A A A A A

Luka 14:25-35
25. Taron mutane mai yawa suna tafiya tare da Yesu, sai ya juya ya ce musu,
26. “Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ʼyaʼyansa, da ʼyanʼuwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.
27. Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.
28. “In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don ya ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin.
29. Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa baʼa,
30. yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’
31. “Ko kuma, wane sarki ne, in zai je yaƙi da wani sarki, ai, yakan fara zama ne, ya duba ya ga, ko da mutane dubu goma, shi zai iya karawa da mai zuwa da dubu ashirin?
32. In ba zai iya ba, to, tun suna nesa, zai aika da wakilai, su je neman sharuɗan salama.
33. Haka nan fa, kowane ne a cikin ku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.
34. “Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa?
35. Ba shi da wani amfani, ko ga ƙasa, ko ga juji, sai dai a zubar da shi. ‘Duk mai kunnen ji, yǎ ji.’ ”