A A A A A

Luka 13:23-35
23. Sai wani ya tambaye shi, ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu,
24. “Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba.
25. Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yǎ daɗe, buɗe mana ƙofa.’ “ Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’
26. “ Saʼan nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’
27. “ Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’
28. “ Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, saʼad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.
29. Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah.
30. Hakika, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.”
31. A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”
32. Ya amma ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci, cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, saʼan nan a rana ta uku in cika burin aikina.
33. Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, saʼan nan in ci gaba da yin haka washegari kuma, gama hakika, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’
34. “ Ya, Urushalima, Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ʼyaʼyanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ʼyaʼyanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!
35. Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”