English
A A A A A

Luka 13:1-22
1. A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya garwaya jininsu tare da jinin hadayunsu.
2. Yesu ya amsa, ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala?
3. Ina gaya muku, aʼa! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.
4. Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya ya fāɗi a kansu a Silowam, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne?
5. Ina gaya muku, aʼa! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”
6. Sai ya faɗa wannan misali, ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ʼyaʼyan itacen, sai ya tarar ba ta yi ʼyaʼya ba.
7. Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ʼyaʼyan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’
8. “ Mutumin ya amsa, ya ce, ‘Ranka yǎ daɗe, ka bar shi, in yi masa ban ƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya.
9. In kuwa ya ba da ʼyaʼya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’ ”
10. Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majamiʼa,
11. a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan.
12. Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ʼyantar da ke daga rashin lafiyarki.”
13. Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.
14. Amma mai mulkin majamiʼar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.”
15. Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, ya kai shi waje ya ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba?
16. Ashe, ba ya kamata a ʼyantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya ɗaure ta ba?”
17. Saʼad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi.
18. Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi?
19. Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.”
20. Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah?
21. Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya garwaye ƙullun duka.”
22. Saʼad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa.