A A A A A

Luka 12:32-59
32. “Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin.
33. Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakunkuna da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za ta kare ba a sama, inda ko ɓarawo ba zai yi kusa ba, ko kuma asu ba za su iya su lalatar ba.
34. Gama inda dukiyarku take, a nan ne zuciyarku ma take.
35. “Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci,
36. kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan.
37. Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, saʼan nan ya yi musu hidimar abinci.
38. Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a cikin saʼa ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne.
39. Amma ku fahimci wannan: Da maigida ya san saʼar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba.
40. Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a saʼar da ba ku yi tsammani ba.”
41. Bitrus ya yi tambaya, ya ce, “Ya Ubangiji, mu ne kake faɗa wa wannan misali, ko kuwa ga kowa da kowa ne?”
42. Ubangiji ya amsa, ya ce, “To wane ne manaja mai aminci da hikima, wanda maigida ya ba shi riƙon bayinsa, domin ya ba su abincinsu a daidai lokaci?
43. Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka.
44. Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa.
45. Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa, ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ saʼan nan ya fara dukan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa.
46. Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a saʼar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya.
47. “Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka.
48. Amma wanda bai sani ba, ya kuwa yi abin da ya isa horo, za a dūke shi kaɗan. Duk wanda aka ba shi mai yawa, mai yawan ne za a bida daga gare shi. Duk wanda kuma aka ba shi riƙon amana mai yawa, fiye da haka kuma za a bida daga gare shi.
49. “Na zo ne domin in kawo wuta a duniya. Ina so da ta riga ta kunnu!
50. Amma ina da baftismar da za a yi mini, na kuwa damu sosai, sai na kammala ta!
51. Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? Aʼa! Ina gaya muku, rabuwa ne.
52. Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun.
53. Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”
54. Ya ce wa taron, “Saʼad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi.
55. Saʼad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi.
56. Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba?
57. “Don me ba ku iya auna wa kanku, abin da yake daidai ba?
58. Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku.
59. Ina gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.”