English
A A A A A

Luka 12:1-31
1. Ana nan saʼad da taron dubban mutane suka taru har suna tattaka juna, Yesu fara yin magana, da farko da almajiransa, ya ce, “Ku yi hankali da yistin Farisiyawa, wato, munafunci.
2. Ba abin da yake rufe da ba za a fallasa ba, ko kuma abin da yake ɓoye da ba za a bayyana ba.
3. Abin da kuka faɗa a cikin duhu, za a ji shi a hasken rana. Kuma abin da kuka faɗa a kunne, a cikin ɗakunan na ciki-ciki, za a yi shelarsa daga kan rufin ɗakuna.
4. “Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi.
5. Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.
6. Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba.
7. Hakika, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.
8. “Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban malaʼikun Allah.
9. Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban malaʼikun Allah.
10. “Kuma duk wanda ya faɗi kalmar zagi a kan Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya saɓa wa Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.
11. “Saʼad da an kai ku a gaban majamiʼu, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa,
12. gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”
13. Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗanʼuwana ya raba gādon da ni.”
14. Yesu ya amsa masa, ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?”
15. Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”
16. Sai ya gaya musu wannan misali, ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai.
17. Ya yi tunani a ransa, ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’
18. “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki.’
19. Ni kuma zan ce wa raina, ‘Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.’
20. “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a bidi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’
21. “Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”
22. Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa.
23. Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.
24. Ku dubi hankaki. Ba sukan yi shuki ko girbi ba, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa!
25. Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, na iya ƙara ko saʼa ɗaya ga rayuwarsa?
26. Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?
27. “Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba.
28. In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, saʼan nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!
29. Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su.
30. Gama duniya ta masu bautar gumaka, da ba ta san Allah ba, tana faman neman dukan irin waɗannan abubuwa. Amma Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.
31. Amma ku bidi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.