A A A A A

Luka 11:29-54
29. Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wata abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana.
30. Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan.
31. A ranar shariʼa, Sarauniyar Kudu za ta tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan.
32. A ranar shariʼa, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba saʼad da Yunana ya yi musu waʼazi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.
33. “Babu wanda yakan ƙuna fitila saʼan nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan alkuki, don masu shiga su ga haske.
34. Idonka shi ne fitilar jikinka. Saʼad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma saʼad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu.
35. Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne.
36. Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.”
37. Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyace shi cin abinci tare da shi. Sai kuwa ya shiga ya zauna a tebur.
38. Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.
39. Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta.
40. Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba?
41. Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta.
42. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na anananku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.
43. “Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majamiʼu, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci.
44. “Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.”
45. Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.”
46. Yesu ya amsa, ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba.
47. “Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su.
48. Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu.
49. Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa, ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’
50. Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,
51. wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.
52. “Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.”
53. Da Yesu ya bar wurin, sai Farisiyawa da malaman dokoki suka fara gaba mai tsanani da shi, kuma suna tsokanansa da tambayoyi.
54. Suna fakonsa, don su kama shi a kan wata magana da zai faɗa.