A A A A A

Luka 11:1-28
1. Wata rana Yesu yana adduʼa a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin adduʼa, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”
2. Sai ya ce musu, “Saʼad da kuke yin adduʼa, ku ce: “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo.
3. Ka ba mu kowace rana abincin yini.
4. Ka gafarta mana zunubanmu, kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi. Kada ka kai mu cikin jaraba.’ ”
5. Saʼan nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, saʼan nan ya je wurinsa da tsakar dare, ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku,
6. domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’
7. Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa, ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’
8. Ina gaya muku, ko da yake ba zai so tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.
9. “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.
10. Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.
11. “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon,
12. ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama?
13. In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ʼyaʼyanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”
14. Saʼad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.
15. Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Beʼelzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.”
16. Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman ya nuna musu wata alama daga sama.
17. Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe.
18. In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Beʼelzebub nake fitar da aljanu.
19. In da ikon Beʼelzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan.
20. Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.
21. “Saʼad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan.
22. Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima.
23. “Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.
24. “Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’
25. Saʼad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye.
26. Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”
27. Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”
28. Yesu ya amsa, ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”