English
A A A A A

Luka 10:25-42
25. Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don ya gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?”
26. Yesu ya amsa, ya ce, “Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”
27. Sai ya amsa, ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’, kuma ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”
28. Yesu ya ce, “Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”
29. Amma domin ya kāre kansa, sai ya tambayi Yesu, ya ce, “Shin, wane ne maƙwabcina?”
30. Yesu ya amsa, ya ce, “Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ʼyan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa duka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa.
31. Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa.
32. Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa.
33. Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa.
34. Ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, saʼan nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.
35. Washegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin, ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’
36. “A ganinka, a cikin waɗannan mutane uku, wane ne maƙwabcin mutumin da ya fāɗi a hannun mafasa?”
37. Masanin dokoki ya amsa, ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Yesu ya ce masa, “Je ka, ka yi haka nan.”
38. Yayinda Yesu da almajiransa suna cikin tafiya, sai ya kai wani ƙauye inda wata mace mai suna Marta ta marabce shi a gidanta.
39. Tana da ʼyarʼuwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana jin maganarsa.
40. Marta kuwa, aikin hidima da ya kamata a yi, ya ɗauke mata hankali, sai ta zo wurin Yesu, ta ce, “Ubangiji, ba ka damu da yadda ʼyarʼuwata ta bar mini aiki ni kaɗai ba? Gaya mata ta taimake ni!”
41. Amma Ubangiji ya amsa, ya ce, “Marta, Marta, hankalinki ya tashi, kuma kina damuwa a kan abubuwa da yawa.
42. Amma abu ɗaya tak ake bukata, Maryamu ta zaɓi abin da ya fi kyau, kuma ba za a raba ta da shi ba.”