A A A A A

Luka 10:1-24
1. Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum sabaʼin da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga.
2. Ya ce musu, “Girbi na da yawa, amma maʼaikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da maʼaikata zuwa gonarsa.
3. Ku tafi! Ina aikanku kamar tumaki cikin kyarketai.
4. Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.
5. “Saʼad da kuka shiga wani gida, ku fara da cewa, ‘Salama a gare ku mutanen gida.’
6. In akwai mutum mai salama a gidan, salamarku za ta kasance tare da shi, in kuwa babu, salamarku za ta koma muku.
7. Ku zauna a wannan gidan, kuna ci kuna shan duk abin da suka ba ku, gama maʼaikaci ya cancanci albashinsa. Kada ku yi yawan sāke masauƙi, daga gida zuwa gida.
8. “Saʼad da kuka shiga garin, kuma aka karɓe ku, ku ci ko mene ne da aka ajiye a gabanku.
9. Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’
10. Amma saʼad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce,
11. ‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’
12. Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.
13. “ ‘Kaitonki, Korasin! Kaitonki, Betsaida!’ Ai, da a ce a Taya da Sidon ne aka yi ayyukan banmamaki da aka yi a cikinku, da tuni sun tuba, suna zama cikin shashan makoki da toka.
14. A ranar shariʼa, za a fi jin tausayin Taya da Sidon fiye da ku.
15. Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? Aʼa, za a hallaka ki.
16. “Shi wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Shi wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma shi wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”
17. Mutum sabaʼin da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.”
18. Sai ya amsa, ya ce, “Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya.
19. Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.
20. Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”
21. A wannan lokaci, Yesu, cike da murna ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na yabe ka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima, da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. I, ya Uba, gama wannan shi ne nufinka mai kyau.
22. “Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.”
23. Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a ɓoye, “Albarka ga idanun da suka ga abin da kuke gani.
24. “Ina faɗa muku, annabawa da sarakuna da yawa sun so su ga abin nan da kuke gani, amma ba su gani ba. Sun so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”