English
A A A A A

Luka 6:1-26
1. A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci.
2. Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?”
3. Yesu ya amsa musu, ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, saʼad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba?
4. Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, saʼan nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?”
5. Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.”
6. A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majamiʼa yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye.
7. Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa.
8. Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya.
9. Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci: a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?”
10. Sai ya kalle su duka, saʼan nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
11. Amma suka fusata, suka fara shawara da junansu a kan abin da za su yi da Yesu.
12. Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yǎ yi adduʼa, ya kuma kwana yana adduʼa ga Allah.
13. Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni:
14. Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗanʼuwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu,
15. Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot,
16. Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.
17. Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga koʼina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku,
18. waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su.
19. Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
20. Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, “Masu albarka ne ku da kuke matalauta, gama mulkin Allah naku ne.
21. Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu, gama za ku ƙoshi. Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu, gama za ku yi dariya.
22. Masu albarka ne saʼad da mutane suka ƙi ku, suka ware ku, suka zage ku, suna ce da ku mugaye, saboda Ɗan Mutum.
23. “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.
24. “Amma kaitonku da kuke da arziki, gama kun riga kun sami taʼaziyyarku.
25. Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu, gama za ku zauna da yunwa. Kaitonku da kuke dariya yanzu, gama za ku yi makoki da kuka.
26. Kaitonku saʼad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku, gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya.