English
A A A A A

Markus 11:1-19
1. Saʼad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa,
2. ya ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a ɗaure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan.
3. In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke yin haka?’ Ku gaya masa cewa, ‘Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ ”
4. Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, ɗaure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan,
5. sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, “Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?”
6. Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su.
7. Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa.
8. Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki.
9. Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna! ” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”
10. “Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!” “Hosanna a can cikin samaniya!”
11. Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.
12. Washegari, da suke barin Betani, Yesu kuwa ya ji yunwa.
13. Da ya hangi wani itacen ɓaure mai ganye, sai ya je domin yǎ ga ko yana da ʼyaʼya. Amma da ya kai can, bai tarar da kome ba sai ganye, domin ba lokacin ʼyaʼyan ɓaure ba ne.
14. Sai ya ce wa itacen, “Kada kowa yǎ ƙara cin ʼyaʼyanka.” Almajiransa kuwa suka ji ya faɗi haka.
15. Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru,
16. ya kuma hana kowa yǎ ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki.
17. Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa: “ ‘Za a kira gidana, gidan adduʼa na dukan alʼummai ba’?? Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ʼyan fashi.’ ”
18. Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
19. Da yamma ta yi, sai suka bar garin.