A A A A A

Markus 10:32-52
32. Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna binsa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi.
33. Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Alʼummai,
34. waɗanda za su yi masa baʼa, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yǎ tashi.”
35. Sai Yaƙub da Yohanna, ʼyaʼyan Zebedi maza suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.”
36. Ya tambaye su, ya ce, “Me kuke so in yi muku?”
37. Suka amsa suka ce, “Ka bar ɗayanmu yǎ zauna a damarka, ɗayan kuma a hagunka, a cikin ɗaukakarka.”
38. Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?”
39. Suka ce, “Za mu iya.” Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, kuma yi muku baftisma da aka yi mini,
40. amma zama a damana ko haguna, ba ni nake ba da izinin ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.”
41. Da sauran goman suka ji wannan, sai suka yi fushi da Yaƙub da Yohanna.
42. Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin alʼummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko.
43. Ba haka ya kamata yǎ zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yǎ zama babba a cikinku, dole yǎ zama bawanku.
44. Duk wanda kuma yake so yǎ zama na farko, dole yǎ zama bawan kowa.
45. Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yǎ yi bauta, yǎ kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
46. Sai suka iso Yeriko. Saʼad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa, (wato, Ɗan Timawus), yana zaune a gefen hanya yana bara.
47. Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
48. Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yǎ yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana, cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”
49. Yesu ya tsaya, ya ce, “Ku kira shi.” Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.”
50. Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.
51. Yesu ya tambaye shi, ya ce, “Me kake so in yi maka?” Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.”
52. Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.