A A A A A

Markus 9:30-49
30. Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yǎ san inda suke ba,
31. domin yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”
32. Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
33. Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su, ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”
34. Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?
35. Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun, ya ce, “In wani yana so yǎ zama na fari, dole yǎ zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”
36. Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yǎ tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu:
37. “Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
38. Yohanna ya ce, “Malam mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, sai muka ce yǎ daina, domin shi ba ɗaya daga cikinmu ba ne.”
39. Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take yǎ faɗi wani abu mummuna game da ni.
40. Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.
41. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.
42. “Da dai wani yǎ sa ɗaya daga cikin waɗannan ʼyan yara masu gaskatawa da ni yǎ yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku.
43. In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.
44. ***
45. In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.
46. ***
47. In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu,
48. inda “ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a iya kashewa.’
49. Za a tsarkake kowa da wuta.