English
A A A A A

Markus 8:22-38
22. Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yǎ taɓa shi.
23. Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi, ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”
24. Sai ya ɗaga kai, ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.”
25. Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai.
26. Yesu ya sallame shi gida, ya ce, “Kada ka shiga cikin ƙauyen. ”
27. Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan da suke kewaye da Kaisariya Filibbi. A hanya ya tambaye su, ya ce, “Wa, mutane suke ce da ni?”
28. Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu Eliya, waɗansu kuma har wa yau sun ce, ɗaya daga cikin annabawa.”
29. Sai ya yi tambaya, ya ce, “Amma ku fa, wa kuke ce da ni?” Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Kiristi. ”
30. Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa kome a kansa.
31. Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yǎ sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yǎ tashi.
32. Ya yi wannan zance a sarari. Sai Bitrus ya jawo shi gefe, ya fara tsauta masa.
33. Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsauta wa Bitrus, ya ce, “Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da alʼamuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”
34. Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa, ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yǎ ƙi kansa, yǎ ɗauki gicciyensa yǎ bi ni.
35. Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.
36. Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?
37. Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa?
38. Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan malaʼiku.”