A A A A A

Luka 5:17-39
17. Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yǎ warkar da masu ciwo.
18. Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu.
19. Da suka ga babu hanyar da za su yi bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.
20. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Aboki, an gafarta maka zunubanka.”
21. Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”
22. Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya, ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?
23. Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?
24. Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”
25. Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.
26. Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”
27. Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.”
28. Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.
29. Sai Lawi ya shirya wa Yesu wani babban liyafa a gidansa. Wani babban taron na masu karɓar haraji, tare da waɗansu suna cin abinci tare da su.
30. Amma Farisiyawa da malaman dokokin da suke a ƙungiyarsu, suka yi wa almajiransa gunaguni, suna cewa, “Don me kuke ci, kuke sha tare da masu karɓar haraji da ‘masu zunubi’?”
31. Yesu ya amsa musu, ya ce, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
32. Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”
33. Suka ce masa, “Almajiran Yohanna sukan yi azumi da adduʼa, haka ma almajiran Farisiyawa, amma naka sai ci da sha.”
34. Yesu ya amsa, ya ce, “Za ku iya sa abokan ango yin azumi yayinda yake tare da su?
35. Amma lokaci yana zuwa, da za a ɗauke ango daga gare su. A waɗancan kwanakin ne za su yi azumi.”
36. Sai ya faɗa musu wannan misali, ya ce, “Ba wanda yakan yage ƙyale daga sabuwar riga ya yi wa tsohuwar riga faci. In ya yi haka, zai yage sabuwar rigar, kuma facin daga sabuwar ba zai dace da tsohuwar rigar ba.
37. Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yǎ zube, salkunan kuma su lalace.
38. Aʼa, sai dai a zuba sabon ruwan inabi a sababbin salkuna.
39. Kuma ba wanda yakan so shan sabon ruwan inabi bayan ya sha tsohon, don yakan ce, ‘Ai, tsohon ya fi kyau.’ ”