English
A A A A A

Luka 5:1-16
1. Wata rana, Yesu yana tsaye a bakin Tafkin Gennesaret, mutane kuma suna ta matsawa kewaye da shi, domin su ji maganar Allah,
2. sai ya hangi jiragen ruwa biyu a bakin tafkin, waɗanda masu kamun kifi suka bari suna wankin tarunsu.
3. Sai ya shiga ɗaya jirgin ruwan da yake na Siman, ya kuma roƙe shi yǎ tura shi kaɗan daga gaci. Sai ya zauna a jirgin ruwan, ya koyar da mutane daga ciki.
4. Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, “Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da tarunka ka kama kifi.”
5. Siman ya amsa, ya ce, “Ranka yǎ daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki tarun.”
6. Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har tarunsu suka fara tsintsinkewa.
7. Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa.
8. Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu, ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!”
9. Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama.
10. Yaƙub da Yohanna, ʼyaʼyan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, “Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”
11. Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.
12. Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi, ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtace ni.”
13. Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin, ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
14. Sai Yesu ya umarce shi, ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”
15. Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.
16. Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yǎ yi adduʼa.