A A A A A

Markus 8:1-21
1. A kwanakin nan wani taro mai girma ya taru. Tun da yake ba su da abin da za su ci, sai Yesu ya kira almajiransa, ya ce,
2. “Ina jin tausayin mutanen nan, kwanansu uku ke nan tare da ni, kuma ba su da abin da za su ci.
3. In na sallame su gida da yunwa, za su kāsa a hanya, don waɗansu daga cikinsu sun zo daga nesa.”
4. Almajiransa suka amsa suka ce, “Amma a ina, a wannan wurin da ba kowa, wani zai iya samun isashen burodi, don a ciyar da su?”
5. Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Burodi guda nawa kuke da su?” Suka ce, “Bakwai.”
6. Sai ya gaya wa taron su zazzauna a ƙasa. Bayan ya ɗauki burodin nan bakwai, ya yi godiya, sai ya kakkarya, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutanen, suka kuwa yi haka.
7. Suna kuma da ƙananan kifi kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu.
8. Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai.
9. Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su,
10. sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.
11. Farisiyawa suka zo suka fara yin wa Yesu tambayoyi. Don su gwada shi, sai suka nemi yǎ nuna musu wata alama daga sama.
12. Sai ya ja numfashi mai zurfi, ya ce, “Don me wannan zamani yake neman ganin abin banmamaki? Gaskiya nake gaya muku, ba wata alamar da za a ba su.”
13. Sai ya bar su, ya koma cikin jirgin ruwan, suka ƙetare zuwa ɗaya hayin.
14. Almajiran suka manta su riƙe burodi, sai dai guda ɗaya da suke da shi a cikin jirgin ruwan.
15. Yesu ya gargaɗe su, ya ce, “Ku yi hankali, ku kuma lura da yistin Farisiyawa da na Hiridus.”
16. Suka tattauna wannan da juna, suna cewa, “Don ba mu da burodi ne.”
17. Da ya gane abin da suke tattaunawa, sai Yesu ya tambaye su, ya ce, “Don me kuke zancen rashin burodi? Har yanzu ba ku gane ko fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne?
18. Kuna da idanu, amma kun kāsa gani, kuna da kunnuwa, amma kun kāsa ji? Ba ku tuna ba?
19. Da na kakkarya burodi guda biyar wa mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka amsa, “Sha biyu.”
20. “Da na kuma kakkarya burodin nan bakwai wa mutum dubu huɗu, kwanduna nawa kuka kwashe cike da gutsattsarin?” Suka ce, “Bakwai.”
21. Ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”