A A A A A

Luka 4:1-30
1. Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada,
2. inda kwana arbaʼin, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.
3. Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yǎ zama burodi.”
4. Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ba da burodi kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”
5. Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya.
6. Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama.
7. Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”
8. Yesu ya amsa, ya ce, “A rubuce yake: ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”
9. Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali, ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa.
10. Gama a rubuce yake: “ ‘Zai umarci malaʼikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau;
11. za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’ ”
12. Yesu ya amsa, ya ce, “An ce: ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’ ”
13. Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.
14. Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu koʼina a ƙauyuka.
15. Ya yi ta koyarwa a majamiʼunsu, kowa kuwa ya yabe shi.
16. Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majamiʼa kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yǎ yi karatu.
17. Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta:
18. “Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta waʼazin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ʼyanci ga ʼyan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ʼyanci ga waɗanda aka danne.
19. In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”
20. Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majamiʼar, suka koma a kansa.
21. Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”
22. Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”
23. Yesu ya ce musu, “Tabbatace, na san za ku faɗa mini karin maganan nan, ‘Likita, warkar da kanka! Ka kuma yi abin da muka ji ka yi a Kafarnahum, a nan garinka.’ ”
24. Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa.
25. “Ina tabbatar muku a zamanin Eliya, akwai gwauraye da yawa a Israʼila, saʼad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani koʼina a ƙasar.
26. Duk da haka, ba a aiki Eliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon.
27. Akwai kuma mutane da yawa a Israʼila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake–sai Naʼaman mutumin Suriyan nan kaɗai.”
28. Dukan mutanen da suke cikin majamiʼa suka fusata ƙwarai da jin wannan.
29. Suka tashi, suka fitar da Yesu bayan gari, suka kai shi goshin tudun da aka gina garin, don su ture shi ƙasa,
30. amma sai ya bi ta tsakiyar taron ya yi tafiyarsa.