A A A A A

Luka 2:25-52
25. To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Israʼila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.
26. An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.
27. Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Saʼad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da alʼadar Doka ta bukaci,
28. sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa:
29. “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.
30. Gama idanuna sun ga cetonka,
31. wanda ka shirya a gaban dukan mutane,
32. haske don bayyanawa ga Alʼummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Israʼila.”
33. Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi.
34. Saʼan nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa: “An ƙaddara yaron nan yǎ zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Israʼila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba,
35. ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”
36. Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,
37. ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da adduʼa.
38. Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.
39. Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.
40. Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.
41. Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.
42. Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga alʼada.
43. Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba.
44. Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Saʼan nan suka fara nemansa cikin ʼyanʼuwansu da abokansu.
45. Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa.
46. Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi.
47. Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa.
48. Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”
49. Sai ya ce, “Don me kuke nema na? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?”
50. Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.
51. Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta.
52. Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.