A A A A A

Luka 2:1-24
1. A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma.
2. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)
3. Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.
4. Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne.
5. Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.
6. Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi,
7. ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.
8. Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare.
9. Sai wani malaʼikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai.
10. Amma malaʼikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.
11. Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.
12. Wannan zai zama alama a gare ku: Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”
13. Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da malaʼikan, suna yabon Allah suna cewa,
14. “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”
15. Da malaʼikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.”
16. Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami.
17. Saʼad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron,
18. duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa.
19. Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta.
20. Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.
21. A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da malaʼika ya ba shi kafin a yi cikinsa.
22. Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji
23. (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji.” ),
24. don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa: “kurciyoyi biyu ko ʼyan tattabarai biyu.”