A A A A A

Luka 1:57-80
57. Saʼad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa.
58. Maƙwabtanta da ʼyanʼuwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.
59. A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne,
60. amma mahaifiyar yaron ta ce, “Aʼa! Za a ce da shi Yohanna.”
61. Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”
62. Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron.
63. Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
64. Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah.
65. Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a koʼina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya.
66. Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.
67. Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci, ya ce:
68. “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Israʼila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.
69. Ya ta da ƙahon ceto dominmu a gidan bawansa Dawuda
70. (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
71. cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu— 
72. don yǎ nuna jinƙai ga kakanninmu, yǎ kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73. rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim:
74. don yǎ kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yǎ kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,
75. cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.
76. “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,
77. don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,
78. saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,
79. don yǎ haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yǎ bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”
80. Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Israʼila.