A A A A A

Luka 1:39-56
39. A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya,
40. inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet.
41. Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki.
42. Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa!
43. Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za ta zo wurina?
44. Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna.
45. Mai albarka ce ita da ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”
46. Sai Maryamu ta ce: “Raina yana ɗaukaka Ubangiji
47. ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
48. gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,
49. gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne.
50. Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani.
51. Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girmankai a zurfin tunaninsu.
52. Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53. Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi.
54. Ya taimaki bawansa Israʼila, yana tunawa yǎ nuna jinƙai
55. ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”
56. Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku saʼan nan ta koma gida.