A A A A A

Luka 1:21-38
21. Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki mene ne ya sa ya daɗe haka a cikin haikali.
22. Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.
23. Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida.
24. Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar.
25. Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.”
26. A wata na shida, sai Allah ya aiki malaʼika Jibraʼilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili,
27. gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu.
28. Malaʼikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.”
29. Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka?
30. Amma malaʼikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.
31. Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu.
32. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar mahaifinsa Dawuda,
33. zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”
34. Maryamu ta tambayi malaʼikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?”
35. Malaʼikan ya amsa, ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.
36. ʼYarʼuwarki Elizabet ma za ta haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida.
37. Gama ba abin da zai gagari Allah.”
38. Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yǎ zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai malaʼikan ya tafi abinsa.