English
A A A A A

Luka 1:1-20
1. Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu,
2. kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara.
3. Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus,
4. don ka san gaskiyar abubuwan da aka koya maka.
5. A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ʼyar zuriyar Haruna ce.
6. Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.
7. Sai dai ba su da ʼyaʼya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.
8. Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah,
9. sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuriʼa, bisa ga alʼadar aikin firist, yǎ shiga haikalin Ubangiji yǎ ƙone turare.
10. Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna adduʼa.
11. Sai malaʼikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare.
12. Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi.
13. Amma malaʼikan ya ce masa: “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji adduʼarka. Matarka Elizabet za ta haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna.
14. Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa,
15. gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.
16. Shi ne zai juye mutanen Israʼila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu.
17. Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Eliya, domin yǎ juye zukatan iyaye ga ʼyaʼyansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya-don yǎ kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.”
18. Sai Zakariya ya tambayi malaʼikan, ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.”
19. Malaʼikan ya ce, “Ni ne Jibraʼilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi.
20. Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”