A A A A A

Markus 7:14-37
14. Sai Yesu ya sāke kiran taron wurinsa, ya ce, “Ku saurare ni dukanku, ku kuma fahimci wannan.
15. Ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi. Sai dai abin da ya fita daga cikin mutum ne, yake ƙazantar da shi.”
16. ***
17. Bayan ya bar taron, ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi maʼanar wannan misali.
18. Ya ce, “Ashe, ba ku da saurin ganewa? Ba ku gane cewa ba abin da yake shiga mutum daga waje ba ne yake ƙazantar da shi.
19. Gama ba ya shiga cikin zuciyarsa, sai dai cikin tumbinsa, saʼan nan kuma yǎ fita daga jikinsa.” (Da faɗin haka, Yesu ya nuna tsabtar kowane irin abinci.)
20. Ya ci gaba: “Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ‘ƙazantar’ da shi.
21. Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,
22. kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen shaʼawa, kishi, ɓata suna, girmankai da kuma wauta.
23. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ‘ƙazantar’ da mutum.”
24. Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa yǎ sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba.
25. Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa.
26. Macen kuwa Baheleniya ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yǎ fitar da aljani da yake jikin diyarta.
27. Yesu ya ce mata, “Da farko, bari ʼyaʼya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”
28. Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci ɓurɓudin da suke fāɗuwa daga abincin yaran.”
29. Sai ya ce mata, “Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”
30. Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
31. Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis.
32. A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yǎ ɗibiya hannunsa a kan mutumin.
33. Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin.
34. Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, saʼan nan ya ce masa, “Effata!” (Wato, “Buɗe!”)
35. Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.
36. Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi.
37. Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”