A A A A A

Markus 15:25-47
25. Saʼa ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.
26. Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, “SARKIN YAHUDAWA.”
27. Suka gicciye ʼyan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
28. ***
29. Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku,
30. sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”
31. Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa baʼa a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!
32. Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Israʼila, yǎ sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.
33. Daga saʼa ta shida har zuwa saʼa ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar.
34. A daidai saʼa ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” Wanda yake nufin, “Ya Allahna, Ya Allahna, don me ka yashe ni?”
35. Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Eliya.”
36. Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yǎ sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Eliya zai zo yǎ saukar da shi.”
37. Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.
38. Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa.
39. Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”
40. Waɗansu mata suna ƙallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yosi, da kuma Salome.
41. A Galili waɗannan mata ne suka riƙa binsa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.
42. Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye, (wato, ana washegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai
43. Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
44. Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.
45. Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.
46. Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, saʼan nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.
47. Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yosi sun ga inda aka kwantar da shi.