A A A A A

Markus 15:1-24
1. Da sassafe, sai manyan firistoci tare da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka ɗaure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.
2. Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa, ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”
3. Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.
4. Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa, ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”
5. Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.
6. Yanzu fa, alʼada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.
7. Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ʼyan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.
8. Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yǎ yi musu abin da ya saba yi.
9. Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
10. Don ya san saboda kishi ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.
11. Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.
12. Bilatus ya tambaye su, ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”
13. Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”
14. Bilatus ya yi tambaya, ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”
15. Don son yǎ faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, saʼan nan ya ba da shi a gicciye.
16. Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.
17. Suka sa masa wata riga mai launin shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.
18. Sai suka fara ce masa, “Ranka yǎ daɗe sarkin Yahudawa!”
19. Suka dinga bugunsa a ka da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa ban girma na baʼa.
20. Bayan da suka gama yin masa baʼa, suka tuɓe rigar mai launin shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
21. Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yǎ ɗauki gicciyen.
22. Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai.)
23. Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yǎ rage zafi, amma bai sha ba.
24. Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuriʼa a kansu don su ga abin da kowa zai samu.