A A A A A

Markus 14:55-72
55. Manyan firistoci da dukan ʼyan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.
56. Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba ta zo ɗaya ba.
57. Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,
58. “Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ”
59. Duk da haka ma, shaidarsu ba ta zo ɗaya ba.
60. Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu, ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”
61. Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa, ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”
62. Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”
63. Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma?
64. Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa.
65. Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.
66. Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin maʼaikatan babban firist, ta zo can.
67. Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”
68. Amma ya yi mūsu, ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.
69. Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.”
70. Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”
71. Sai ya fara laʼantar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”
72. Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa, cewa: “Kafin zakara yǎ yi cara sau biyu: za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.