English
A A A A A

Markus 14:27-54
27. Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce, cewa: “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’
28. Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”
29. Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”
30. Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau-I, da daren nan-kafin zakara yǎ yi cara sau biyu kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”
31. Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi, ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
32. Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi adduʼa.”
33. Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.
34. Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”
35. Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi adduʼa, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan saʼa.
36. Ya ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”
37. Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na saʼa ɗaya?
38. Ku yi tsaro, ku kuma yi adduʼa, domin kada ku fāɗi cikin jaraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
39. Ya sāke komawa, ya maimata adduʼar da ya yi.
40. Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.
41. Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi.
42. Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!”
43. Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.
44. Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su, cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.”
45. Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu, ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba.
46. Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi.
47. Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist.
48. Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni?
49. Kowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.”
50. Sai kowa ya yashe shi ya gudu.
51. Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi,
52. sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara.
53. Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.
54. Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.