English
A A A A A

Markus 14:1-26
1. To, Bikin Ƙetarewa da kuma Bikin Burodi Marar Yisti kuwa sun rage kwana biyu a yi, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suna neman wani dalilin kawai su kama Yesu, su kashe.
2. Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”
3. Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutum da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tandu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tandun, ta kuma zuba turaren a kansa.
4. Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, cikin fushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka?
5. Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi na shekara guda, kuɗin kuma a ba wa matalauta. Sai suka tsauta mata cikin fushi.”
6. Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.
7. Matalauta kam suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.
8. Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin janaʼizata.
9. Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi waʼazin bishara koʼina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”
10. Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun, ya je wajen manyan firistoci don yǎ bashe Yesu a gare su.
11. Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafin ba da shi.
12. A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga alʼada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu yi maka shirin cin Bikin Ƙetarewa?”
13. Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa, ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.
14. Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya: Ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’
15. Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”
16. Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
17. Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun.
18. Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”
19. Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatace, ba ni ba ne, ko?”
20. Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano.
21. Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”
22. Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”
23. Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.
24. Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.
25. Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ʼyaʼyan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”
26. Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.