English
A A A A A

Markus 13:21-37
21. A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata.
22. Domin Kiristi na ƙarya masu yawa, da annabawan ƙarya za su fiffito, su kuma aikata alamu da ayyukan banmamaki, don su ruɗi zaɓaɓɓu, in zai yiwu.
23. Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.
24. “Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan, “ ‘rana za ta yi duhu, wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
25. taurari za su fāffāɗo daga sararin sama. Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’
26. “A saʼan nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai, da iko, da ɗaukaka mai girma.
27. Zai kuma aiko malaʼikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yǎ zuwa iyakar sama.
28. “To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan.
29. Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana dab da bakin ƙofa.
30. Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru.
31. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.
32. “Game da wannan rana ko saʼa kuwa, ba wanda ya sani, ko malaʼikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai Uban kaɗai.
33. Ku yi zaman tsaro! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba.
34. Yana kama da mutumin da zai yi tafiya: Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka ba shi, yǎ kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yǎ yi tsaro.
35. “Saboda haka, sai ku yi zaman tsaro, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba--ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne.
36. In ya zo kwaram, kada ka bari yǎ tarar da kai kana barci.
37. Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa: ‘Ku yi tsaro!’ ”