A A A A A

Markus 13:1-20
1. Da yake barin haikalin, ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manyan manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan mana masu kyau!”
2. Yesu ya amsa, ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.”
3. Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce,
4. “Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za ta nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”
5. Sai Yesu ya ce musu: “Ku lura fa kada wani yǎ ruɗe ku.
6. Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
7. Saʼad da kuka ji labaran yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yǎ tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.
8. Alʼumma za ta tasar wa alʼumma, mulki kuma yǎ tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.
9. “Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majamiʼu. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.
10. Dole sai an fara yin waʼazin bishara ga dukan alʼummai.
11. Saʼad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shariʼa, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
12. “Ɗanʼuwa zai ba da ɗanʼuwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ʼYaʼya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
13. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
14. “Saʼad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’ tsaye inda bai kamata ba--mai karatu ya gane-to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.
15. Kada wani da yake kan rufin gidansa yǎ sauka, ko yǎ shiga gida don yǎ ɗauki wani abu.
16. Kada wani da yake gona kuma yǎ koma don ɗaukar rigarsa.
17. Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ʼyaʼya a waɗancan kwanakin!
18. Ku yi adduʼa, kada wannan yǎ faru a lokacin sanyi.
19. Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irin ba tun farkon halitta, har yǎ zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.
20. Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin.