English
A A A A A

Markus 12:28-44
28. Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi, ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”
29. Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan: ‘Ya ku Israʼila, ku saurara, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.
30. Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’
31. Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan.”
32. Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi.
33. Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”
34. Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.
35. Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya, ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne?
36. Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina: “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’
37. Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya kuwa zai zama ɗansa?” Taro mai yawa suka saurare shi da murna.
38. Saʼad da Yesu yake koyarwa, ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci.
39. Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majamiʼu, da kuma wuraren zaman manya a bukukuwa.
40. Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen adduʼoʼi. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.”
41. Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin baitulmalin haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa.
42. Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo.
43. Yesu ya kira almajiransa wurinsa, ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin baitulmalin nan ya fi na sauran dukan.
44. Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba kome-duk abin da take da shi na rayuwa.”