A A A A A

Markus 12:1-27
1. Saʼan nan ya fara yi musu magana da misalai, ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsen inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, saʼan nan ya yi tafiya.
2. Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ʼyan hayan, don yǎ karɓo masa ʼyaʼyan inabin daga wurinsu.
3. Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi.
4. Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi.
5. Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.
6. “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’
7. “Amma ʼyan hayan suka ce wa juna, Aha! ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yǎ zama namu.’
8. Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.
9. “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yǎ karkashe dukan ʼyan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin.
10. Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba: “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.
11. Ubangiji ya yi wannan, ya kuma yi kyau a idanunmu’?”
12. Sai suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, sai suka bar shi suka yi tafiyarsu.
13. Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hirudus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa.
14. Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin raʼayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu?
15. Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya, ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”
16. Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?” Suka ce, “Na Kaisar.”
17. Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.” Suka yi mamakinsa ƙwarai.
18. Saʼan nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya.
19. Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗanʼuwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ʼyaʼya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yǎ kuma samo wa ɗanʼuwansa ʼyaʼya.
20. To, an yi waɗansu ʼyanʼuwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ʼyaʼya.
21. Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ʼyaʼya. Haka kuma na ukun.
22. A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ʼyaʼya. Daga ƙarshe, macen ta mutu.
23. To, a tashin matattu, matar wa za ta zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”
24. Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah?
25. Saʼad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda malaʼiku suke a cikin sama.
26. Game da tashin matattu kuwa-ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi, ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?
27. Shi ba Allah na matattu ba ne, sai dai na masu rai. Kun yi mummunan kuskure!”