A A A A A

Markus 11:20-33
20. Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa.
21. Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, “Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka laʼanta, ya yanƙwane!”
22. Yesu ya amsa, ya ce, “Ku gaskata da Allah.
23. Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.
24. Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin adduʼa, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.
25. A duk lokacin da kuke tsaye cikin adduʼa, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yǎ gafarta muku zunubanku.
26. Amma in ba ku gafartawa, Ubanku da yake cikin sama, ba zai gafarta muku zunubanku ba.”
27. Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa.
28. Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”
29. Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.
30. Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!”
31. Sai suka tattauna da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’
32. In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’….” (Suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.)
33. Don haka, suka amsa wa Yesu cewa, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”