English
A A A A A

Markus 7:1-13
1. Farisiyawa da waɗansu malaman dokoki waɗanda suka zo daga Urushalima, suka taru kewaye da Yesu.
2. Sai suka ga waɗansu daga cikin almajiransa suna cin abinci da hannuwa “marasa tsabta,” wato, da ba a wanke ba.
3. (Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci, sai sun wanke hannuwa sarai tukuna, yadda alʼadun dattawa suka ce.
4. Saʼad da suka dawo daga wurin kasuwanci, dole su wanke hannu kafin su ci abinci. Sukan kuma kiyaye waɗansu alʼadu da yawa, kamar wanken kwafuna, tuluna da butoci. )
5. Saboda haka, Farisiyawa da malaman dokoki suka tambayi Yesu, suka ce, “Don me almajiranka ba sa bin alʼadun dattawa, a maimakon haka suna cin abinci da hannuwa ‘marasa tsabta’?”
6. Ya amsa, ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa: “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.
7. A banza suke mini sujada, koyarwarsu dokokin mutane ne kawai.’
8. Kun bar umarnan Allah, kuna bin alʼadun mutane.”
9. Ya kuma ce musu, “Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye alʼadunku!
10. Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’  kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’
11. Amma ku, kukan ce, in mutum ya ce wa mahaifinsa, ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da ya kamata ku samu daga wurina, Korban ne,’ (wato, abin da aka keɓe wa Allah),
12. ta haka ba kwa ƙara barinsa yǎ yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa wani abu.
13. Ta haka kuke rushe maganar Allah ta wurin alʼadun da kuke miƙa wa ʼyaʼyanku. Haka kuma kuke yin abubuwa da yawa.”