A A A A A

Mattiyu 25:1-30
1. “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.
2. Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.
3. Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.
4. Masu hikimar kuwa suka riƙo kwalaben mai da fitilunsu.
5. Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.
6. “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’
7. “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.
8. Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’
9. “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘Aʼa, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’
10. “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.
11. “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yǎ daɗe! Ranka yǎ daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’
12. “Amma ya amsa, ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’
13. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko saʼar ba.
14. “Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa.
15. Ga guda, ya ba shi talentii biyar na kuɗi, ga wani talentii biyu, ga wani kuma talentii ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Saʼan nan ya yi tafiyarsa.
16. Mutumin da ya karɓi talentii biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talentii biyar.
17. Haka ma, wannan mai talentii biyu, shi ma ya yi riba biyu.
18. Amma mutumin da ya karɓi talentii ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.
19. “Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su.
20. Mutumin da ya karɓi talentii biyar, ya kawo ƙarin talentii biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talentii biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’
21. “Maigidansa ya amsa, ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
22. “Mutumin da yake da talentii biyu, shi ma ya zo, ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talentii biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’
23. “Maigidansa ya amsa, ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
24. “Saʼan nan mutumin da ya karɓi talentii ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan shaʼani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba.
25. Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentiinka a ƙasa. Ga abinka.’
26. “Maigidansa ya amsa, ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba?
27. To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don saʼad da na dawo da na karɓi abina da riba.
28. “ ‘Karɓi talentiin daga hannunsa ku ba wanda yake da talentii goma.
29. Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.
30. Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’