A A A A A

Mattiyu 24:29-51
29. “Nan da nan bayan tsabar wahalan nan, “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su faffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
30. “A saʼan nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan alʼumman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.
31. Zai kuwa aiki malaʼikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.
32. “Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure: Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa.
33. Haka kuma, saʼad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana dab da bakin ƙofa.
34. Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru.
35. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta taɓa shuɗe ba.
36. “Babu wanda ya san wannan rana ko saʼa, ko malaʼikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.
37. Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.
38. Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi;
39. ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.
40. Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.
41. Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.
42. “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba.
43. Sai dai ku gane wannan: Da maigida ya san ko a wane lokaci ne na dare, ɓarawo zai zo, da sai yǎ zauna a faɗake yǎ kuma hana a shiga masa gida.
44. Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a saʼar da ba ku zata ba.
45. “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yǎ lura da bayi a cikin gidansa, yǎ riƙa ba su abinci a daidai lokaci?
46. Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka.
47. Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yǎ lura da dukan dukiyarsa.
48. Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’
49. Saʼan nan yǎ fara dūkan ʼyanʼuwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya.
50. Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba kuma a saʼar da bai sani ba.
51. Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yǎ kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.