A A A A A

Mattiyu 24:1-28
1. Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya saʼad da almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali.
2. Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”
3. Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”
4. Yesu ya amsa: “Ku lura fa, kada wani yǎ ruɗe ku.
5. Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
6. Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yǎ tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.
7. Alʼumma za ta tasar wa alʼumma, mulki yǎ tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.
8. Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.
9. “Saʼan nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan alʼummai za su ƙi ku saboda ni.
10. A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,
11. annabawan ƙarya da yawa kuma za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.
12. Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za ta yi sanyi,
13. amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
14. Za a kuma yi waʼazin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yǎ zama shaida ga dukan alʼummai, saʼan nan ƙarshen yǎ zo.
15. “Saboda haka saʼad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’ wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a Wuri mai tsarki-mai karatu yǎ gane— 
16. to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu.
17. Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yǎ sauko don ɗaukar wani abu a gida.
18. Kada wani da yake gona kuma yǎ komo don ɗaukar rigarsa.
19. Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ʼyaʼya a waɗancan kwanakin!
20. Ku yi adduʼa, kada gudunku yǎ zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.
21. Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har zuwa yanzu-ba kuwa za a ƙara yi ba.
22. Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.
23. A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata.
24. Gama Kiristi masu yawa na ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma-in zai yiwu.
25. Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.
26. “Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata.
27. Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.
28. Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.