A A A A A

Mattiyu 23:23-39
23. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku-naʼanaʼa, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki-adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.
24. Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi.
25. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai.
26. Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, saʼan nan bayan ma zai zama da tsabta.
27. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta.
28. Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta.
29. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado.
30. Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’
31. Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne.
32. To, sai ku cikasa zunubin kakanninku!
33. “Ku macizai! ʼYaʼyan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta?
34. Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majamiʼunku kuna kuma binsu gari gari.
35. Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.
36. Gaskiya nake gaya muku, duk wannan zai auko wa wannan zamani.
37. “Ayya Urushalima, Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ʼyaʼyanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ʼyaʼyanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi.
38. Ga shi, an bar muku gidanku a yashe.
39. Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba sai kun ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”