A A A A A

Mattiyu 23:1-22
1. Saʼan nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa:
2. “Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa.
3. Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke waʼazi.
4. Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.
5. “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani: Sukan yi layunsu fantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;
6. suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba gaba a majamiʼu;
7. suna so a yi ta gaisuwansu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’
8. “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ʼyanʼuwa ne.
9. Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba’, gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama.
10. Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi.
11. Mafi girma a cikinku, zai zama bawanku.
12. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.
13. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kun rufe mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba.
14. ***
15. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, saʼad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu.
16. “Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’
17. Wawaye makafi! Wanne ya fi girma: zinariyar, ko haikalin da yake tsarkake zinariyar?
18. Kukan kuma ce, ‘In wani ya rantse da bagade, ba damuwa; amma in ya rantse da bayarwar da take bisansa, sai rantsuwar ta kama shi.’
19. Makafi kawai! Wanne ya fi girma: bayarwar, ko kuwa bagaden da yake tsarkake bayarwar?
20. Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagade, ya rantse ne da bagaden tare da abin da yake bisansa.
21. Kuma duk wanda ya rantse da haikali, ya rantse ne da shi da kuma wanda yake zaune a cikinsa.
22. Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa.