English
A A A A A

Mattiyu 22:23-46
23. A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya.
24. Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ʼyaʼya, dole ɗanʼuwansa yǎ auri gwauruwar yǎ kuma haifar wa ɗanʼuwan ʼyaʼya.
25. A cikinmu an yi ʼyanʼuwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ʼyaʼya ba, sai ya bar matarsa wa ɗanʼuwansa.
26. Haka ya faru da ɗanʼuwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai.
27. A ƙarshe, macen ta mutu.
28. To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za ta zama, da yake dukansu sun aure ta?”
29. Yesu ya amsa, ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.
30. Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar malaʼiku a sama.
31. Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu-ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne,
32. ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, sai dai na masu rai.”
33. Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
34. Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru.
35. Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya:
36. “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”
37. Yesu ya amsa, ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’
38. Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma.
39. Ta biye kuma kamar ta farkon take: ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
40. Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”
41. Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,
42. “Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.”
43. Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,
44. “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina: “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’
45. To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?”
46. Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.