English
A A A A A

Mattiyu 22:1-22
1. Yesu ya sāke yi musu magana da misalai, yana cewa:
2. “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.
3. Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.
4. “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi, ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci: An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’
5. “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu-ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.
6. Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.
7. Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.
8. “Saʼan nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.’
9. Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.
10. Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.
11. “Amma da sarkin ya shigo don yǎ ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.
12. Ya yi tambaya, ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.
13. “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku ɗaure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’
14. “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”
15. Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.
16. Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hirudus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.
17. To, ka gaya mana, a raʼayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko aʼa?”
18. Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?
19. Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,
20. sai ya tambaye su, ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”
21. Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
22. Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.