A A A A A

Markus 6:30-56
30. Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar.
31. To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”
32. Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa.
33. Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can.
34. Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.
35. A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure.
36. Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”
37. Sai ya amsa, ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”
38. Sai ya yi tambaya, ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.” Da suka duba, sai suka ce, “Biyar-da kifi biyu.”
39. Saʼan nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa.
40. Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin.
41. Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka.
42. Kowa ya ci, ya ƙoshi,
43. almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu.
44. Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.
45. Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yǎ sallami taron.
46. Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yǎ yi adduʼa.
47. Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai.
48. Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su,
49. amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu,
50. domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata. Nan da nan ya yi magana da su, ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”
51. Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki,
52. gama ba su fahimci alʼamarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.
53. Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka ɗaure jirgin a ƙugiya.
54. Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu.
55. Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake.
56. Duk inda ya shiga-cikin ƙauyuka, birane ko karkara-sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yǎ bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.