English
A A A A A

Markus 6:1-29
1. Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa.
2. Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majamiʼa, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki. Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka!
3. Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗanʼuwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ʼyanʼuwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.
4. Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ʼyanʼuwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.”
5. Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su.
6. Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu. Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa.
7. Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.
8. Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda-ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku.
9. Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.
10. Duk saʼad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin.
11. In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku saʼad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”
12. Suka fita, suna yi waʼazi, suna ce wa mutane su tuba.
13. Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.
14. Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a koʼina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”
15. Waɗansu suka ce, “Ai, Eliya ne.” Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.”
16. Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!”
17. Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka ɗaure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗanʼuwansa Filibus, wadda ya aura.
18. Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗanʼuwanka.”
19. Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba ta iya ba,
20. domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk saʼad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yǎ ji shi.
21. A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili.
22. Saʼad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa. Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.”
23. Ya yi mata alkawari da rantsuwa, cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”
24. Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?” Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.”
25. Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon: “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu yanzun nan.”
26. Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yǎ hana ta ba.
27. Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku.
28. Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta.
29. Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari.